Sabon koci ya zabi sabbin 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabon kocin ya ce ya ajiye wasu 'yan wasa ne ba don rashin kwarewa ba, sai don ba su da zimma a wannan lokaci

Sabon kocin Afirka ta kudu Ephraim Mashaba ya fitar da jerin 'yan wasansa na farko da za su buga wasan samun damar shiga gasar cin kofin Afirka da za a fara a makon gobe.

Ranar 5 ga watan Satumba kungiyar Bafana Bafana za ta kara da Sudan, bayan kwana biyar kuma za ta karbi bakuncin zakarun Afirka Nijeriya.

An yi mamakin rashin ganin dan wasan tsakiya na Ajax, Thulani Serero a sahun 'yan wasan na mutum 25, haka kuma, babu Siphiwe Tshabalala da Bernard Parker saboda suna fama da rauni.

Mashaba ya ce abun burgewa ne zabar ayarin 'yan wasan kasa, ko da yake abu ne mai wuya, musammam a lokacin da kasar ke da kwararrun 'yan wasa a kowanne bangare. Ya ce gaskiya akwai hazikan 'yan wasa a Afirka ta kudu.

Ya ce ya sanya matasan 'yan wasa a cikin kungiyar ne don tanadin gaba.

'yan wasan:

Masu tsaron gidai: Itumeleng Khune, Senzo Meyiwa da Dumisani Msibi

'Yan baya: Anele Ngcongca, Ayabulela Magqwaka, Sibusiso Khumalo, Thulani Hlatshwayo, Buhlebuyeza Mkhwanazi, Erick Mathoho, Thabo Matlaba, Rivaldo Coetzee, Ramahlwe Mphahlele

'Yan tsakiya: Themba Zwane, Sibusiso Vilakazi, Oupa Manyisa, Andile Jali, Dean Furman, Ayanda Patosi, Mandla Masango, Keagan Dolly, Kamohelo Mokotjo

'Yan gaba: Tokelo Rantie, Bongani Ndulula, Bonginkosi Ntuli, David Zulu