Za a duba lafiyar Balotelli a Ingila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Balotelli ya yi kaurin suna wajen janyo rigima a wajen fili ciki har da sa-in-sar da ya yi da tsohon kocinsa Mancini

Za a duba lafiyar dan wasan gaba na AC Milan Mario Balotelli a Ingila yayin da ake ci gaba da tattaunawa a kan kudurin Liverpool na sayen dan wasan a kan fam miliyan 16.

Idan ciniki ya fada, Liverpool za ta dinga biyan dan wasan mai shekaru 24 kimanin fam dubu 120 duk mako.

Sai dai ba lallai ne a kammala cinikin a kan lokaci ba, ta yadda dan wasan zai iya buga karawar da Liverpool za ta yi da tsohuwar kungiyarsa Manchester City a ranar litinin.

An fahimci cewa Liverpool ta daddale da Balotelli a kan kudurinsa wajen dagewa a lokacin buga wasa da kuma kyautata halayyarsa.

Balotelli ya yi wasa a Manchester City tsawon kaka uku daga 2010 zuwa 2013, inda ya jefa kwallaye 20 a raga.

Yana da tagomashi a wajen magoya bayan Man City, inda ya taimaka wa kungiyar wajen lashe gasar Firimiya ta farko tun cikin 1968.