QPR ta gayyaci Paul Gascoigne

Image caption 'Yarsa Bianca ta ce tana fata mahaifinta zai taimaki kansa ya karbi wannan tayi

Kocin QPR Harry Redknapp ya gayyaci tsohon dan wasan tsakiyar Ingila, Paul Gascoigne don ya je ya taimaka masa wajen horas da matasan 'yan wasansa.

Gascoigne, mai shekaru 47, yana da tarihin rashin lafiya, kuma rahotanni sun ce jami'an kula da lafiya na gaggawa sun dauke shi a juma'ar nan daga gidansa na Dorset.

Redknapp wanda ke zaune a kusa da gidan Gascoigne, ya ce idan yana so, ina iya zuwa na dinga daukarsa a kan titi don kai shi wajen aiki.

Hotuna a jaridu da dama na ranar juma'a sun nuna Gascoigne a kanjame kusan da kyar ake iya gane shi daga kamanninsa a lokacin yana wasa.

Masu amfani da shafin Twitter sun aika sakwannin juyayi da goyon baya ga 'yarsa Bianca, wadda ta mayar da amsa a shafin inda ta nuna godiya a kan kalaman kirki da aka aika mata.

Ta ce zan so idan zai yi wannan aiki, gayyata ce a gare shi. Ta ce "Ina ganin Gazza akai-akai, ina kaunarsa, mutum ne mai halin kirki.

Gascoigne na da shekaru 17 lokacin da ya fara buga wasansa na farko a Newscastle cikin 1985, kafin ya koma Tottenham a 1988 a kan fam miliyan 2.3