'Ba tabbas kan Keshi a Super Eagles'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Stephen Keshi ya nuna alamun zai kara gaba

Bisa dukkan alamu Stephen Keshi ba zai koma matsayinsa na kocin Nigeria ba, sakamakon rashin jituwa tsakaninsa da hukumar kwallon kasar watau NFF.

Kwangilar Keshi ta kare a ranar 30 ga watan Yuni, jim kadan bayan da Nigeria ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya, amma kuma sun kasa sasantawa game da kulla sabuwar yarjejeniya.

Keshi ya shaidawa BBC cewar "Bai kamata a dunga jan kafa kan batun yarjejeniya ba, ba zan iya kara jira ba, NFF ta ki ta maida hankali."

Tun a watan Yuli hukumar kwallon Nigeria ta shiga cikin matsala inda aka cire shugaban ta Aminu Maigari, kafin hukumar Fifa ta maido da shi.

Bayanai sun nuna cewar hukumar NFF ta baiwa Keshi sabuwar kwangila ta shekaru hudu a kan dala dubu 30 a duk wata amma kuma yanason a bashi karin kudi kafin ya sanya hannu a kan sabuwar kwangila.

Karin bayani