Barcelona za ta fara kaka ba Neymar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sai dai babu bayani ya zuwa yanzu a kan ko tsawon kwana nawa Neymar zai yi yana jinya

Mai yiwuwa ciwon idon sawu ya hana dan wasan gaba na Barcelona Neymar buga karawar farko da za ta yi a gasar La Liga da kungiyar Elche ranar lahadi.

Dan wasan na kasar Brazil mai shekaru 22 ya jefa biyu daga cikin kwallaye shida a karawar da Barcelona ta casa Leon ta Mexico a wasannin share fagen shiga kaka ranar litinin.

Sai dai, kasa da mako guda bayan likitoci sun ba shi tabbacin warkewa sarai daga raunin da ya ji a gasar cin kofin duniya, sai ga shi Neymar ya kuma jin ciwo a idon sawu.

Barcelona za ta fara kakar bana da sabon koci Luis Enrique wanda ya yi sauye-sauye a jerin 'yan wasan kungiyar sakamakon kammala kakar wasanni a karon farko ba tare da cin wani kwakkwaran kofi ba tsawon shekaru shida.

Rahotanni sun ce kungiyar ta biya fam miliyan 75 don sayen dan wasan gaba na Liverpool Luis Suarez, ko da yake daga baya Barcelona ta ce kudin da ta biya bai fi fam miliyan 65 ba, a lokaci guda kuma ta sayo dan wasan bayan Arsenal Thomas Vermaelen a kan fam miliyan 15.