Kamaru ba ta gayyaci Eto'o wasa ba

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Eto'o ba shi da kulob tun sanda Chelsea ta sallame shi

Kocin Cameroon Volker Finke ya ki ya gayyaci Samuel Eto'o tare da wasu 'yan wasan kasar 13 daga cikin wadanda suka buga wa Kamaru gasar cin kofin Duniya da aka kammala a Brazil.

Kamaru dai za ta ziyarci Jamhuriyar Congo ranar 6 ga watan Satumba, kafin ta karbi bakunci Ivory Coast kwanaki hudu tsakani.

Sai dai kocin wanda Kamaru ta amince masa ya ci gaba da horas da tawagar kasar bayan kofin Duniya, ya gayyato 'yan wasa 25 da za su buga wasan neman tikitin shiga kofin Nahiyar Afirka ranar Asabar.

Sauran fitattun 'yan wasan Kamaru da kocin bai gayyace su ba sun hada da Alex Song da Henri Bedimo wanda ya ke jinyar rauni, da Benoit Assou Ekotto, wanda ya yi kokarin fada da abokin wasansa Benjamin Moukandjo a gasar cin kofin Duniya.