Enyimba ta doke Taraba Fc 3-0

Enyimba Fc Hakkin mallakar hoto Enyimba FC web site
Image caption Enyimba ta hada maki 40 tana kuma matsayi na uku.

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International ta doke Taraba Fc da ci 3-0 a gasar cin kofin Premier Nigeria wasan mako na 25 da suka buga ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Elkanemi Warriors ta doke Bayelsa United da ci 2-0, inda Kaduna United ta lashe Lobi Stars da ci daya mai ban haushi.

Wasan Nembe da Akwa United tashi su kayi kowa yana nema, Warri Wolves kwallaye biyu da nema aka zura mata a gidan Giwa Fc, Nasarawa ta doke Heartland da ci daya mai ban haushi.

Tun a ranar Asabar Kano Pillars ta doke Abia Warriors da ci daya da nema, Gombe United ta zura wa Crown Fc kwallaye biyu da nema, Sunshine ta doke Rangers 2-1, wasan hamayya tsakanin Dolphins da Sharks suka tashi wasa kowa yana nema.

Har yanzu Kano Pillars ce ke matsayi na daya a teburi da maki 43, sai Nasarawa United a matsayi na biyu da maki 41, inda Enyimba na da maki 40 a matsayi na uku.