Khedira zai ci gaba da tamaula a Madrid

Samir Khedira Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Khedira zai ci gaba da buga kwallo a Madrid a bana

Dan kwallon Real Madrid Sami Khedira zai ci gaba da buga tamaula a Bernabeu a kakar wasan bana in ji kocin kulob din Carlo Ancelotti.

An yi ta rade-radin cewa dan kwallon na Jamus mai shekaru 27, zai koma wasa a kungiyar Arsenal ko Bayern Munich, bayanda Ancelotti ya sanar da cewar dan kwallon ya ki sabunta kwantiraginsa da Madrid.

Ancelotti ya kuma sanar da cewa Angel Di Maria mai shekaru 26, ya yi ban kwana da 'yan wasan Madrid, a shirinsa na koma wa kulob din Manchester United.

Real Madrid ta dauko 'yan kwallo da suka hada da James Rodriguez da Toni Kroos a bana, za kuma ta fara gasar cin kofin La Liga da Cordoba ranar Litinin.