An dakatar da koci Simeone wasanni 8

Diego Simeone Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin zai yi zaman hukuncin rashin jagorantar wasanni 8

An dakatar da Kocin Atletico Madrid Diego Simeone jagorantar tsawon wasanni takwas a Spaniya, sakamakon samunsa da rashin da'a a wasan Super Cup karawa ta biyu.

Simeone, mai shekaru 44, ya yi cacar baki da alkalin wasa mai jiran kar ta kwana, har ma ya dan bugi alkalin a baya da kansa a lokacin da suka doke Madrid da ci 1-0.

Hukumar kwallon kafar Spaniya ta same shi da aikata laifukan rashin da'a daban daban har karo hudu a wasan.

Mataimakin koci German Burgos ne zai maye gurbin Simeone a tsawon zaman hukuncin da zai yi.