Liverpool ta kammala daukar Balotelli

Mario Balotell Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Balotelli ya ce ya yi murnar komawa wasaIngila

Kulob din Liverpool ya kammala dauko dan wasan AC Milan Mario Balotelli kan kudi fam miliyan 16.

Tsohon dan kwallon Manchester City mai shekaru 24, ya amince da kwantiragi mai tsawo da kulob din, sai dai ba zai buga a karawar da kungiyar za ta yi ba da City ranar Litinin.

Balotelli ya bar Manchester City, kungiyar da ya buga wa wasa shekaru uku, ya kuma zura kwallaye 30 a raga, a tsawon watanni 17 baya.

Dan wasan ya ce "Na yi farin cikin koma wa Liverpool, an dade ana rade-radi, yanzu kuma zancen ya zama gaskiya".

"Liverpool fitacciyar kungiya ce a Duniya, kuma buga tamaula a Ingila yana da alfanu matuka".