Manchester City ta doke Liverpool 3-1

Man City Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man City ta daura damarar kare kambunta a gasar bana

Mai rike da kofin Premier Ingila Manchester City ta doke Liverpool da ci 3-1 a gasar cin kofin Premier wasan mako na biyu a Ettihad da suka kara ranar Litinin.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Stevan Jovetic lokacin da ya samu kwallo a kuskuren da dan wasan Liverpool ya yi Alberto Moreno.

Jovetic ya kara kwallo ta biyu lokacin da ya samu tamaula ta hannun Samir Nasri, kafin Sergio Aguero ya kara kwallo ta uku da ya samu kwallo ta hannun Jesus Navas.

Daf a tashi wasa Liverpool ta rage kwallo daya, lokacin da Pablo Zabaleta ya ci kansu da kansa.

Sabon dan kwallon da Liverpool ta dauko Mario Ballotelli kan kudi fam miliyan 16 ya kalli wasan a Ettihad.