La Liga: Ronaldo zai buga wa Madrid

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya samu sauki da zai iya buga wasa a yau

Cristiano Ronaldo zai fara buga wa Madrid kwallo a karawar da za suyi da Cordoba a gasar kofin La liga, duk da jinyar rauni da ya yi fama da shi kafin fara gasar bana.

Sai sauya dan kwallon Portugal aka yi a karawar da Atletico Madrid ta doke su a Super Cup ranar Juma'ar da ta wuce.

Kocin kulob din Carlo Ancelotti ya ce "Ya yi atisaye da 'yan wasa cikin koshin lafiya, kuma a shirye Ronaldo yake ya buga karawar da za muyi da Cordoba an jima".

Cristiano, mai shekaru 29, ya ji rauni a bayansa lokacin da suka buga wasan cin Super Cup da Atletico a karawar farko a ranar Talata da suka ta shi 1-1.

Madrid ta barar da damarta a bara, lokacin da abokiyar hamayyarta Atletico ta doke ta kuma lashe kofin La Liga wanda rabonta da kofin tun shekarar 1996.