Keshi zai jagoranci Nigeria wasanni 2

Stephen Keshi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin na fatan zama domin tsawaita kwantiraginsa

Stephen Keshi zai dauki tawagar Super Eagles buga wasan neman damar shiga gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da za a yi a Morocco.

Kwantiragin Keshi da Najeriya ya kare ne a karshen watan Yuni, kuma karshen makon jiya ya ce ya gaji da jiran gawon shanun ranar da za a tsawaita kwantiraginsa.

Sai dai a yanzu ya yanke shawarar horas da kungiyar na kwarya-kwaryan lokaci, kafin ya san makomarsa dangane da aikin.

Keshi ya ce "Na girmama kiraye-kirayen 'yan kasata da kuma rokon da ministan wasanni ya yi mini da cewa na jagoranci tawagar Super Eales wasanni biyu".

Kocin ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da gidan talabijin na Nigeria ranar Litinin ce wa "Sun yi aiki tukuru kafin su lashe kofin Nahiyar Afirka, ya kamata su dora domin su kare kambunsu a Morocco".

Nigeria za ta karbi bakuncin Congo ranar 6 ga watan Satumba, kafin ta ziyarci Bafana-Bafana na Afirka ta kudu kwanaki hudu tsakani.