United ta amince da farashin Di Maria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Angel Di Maria

Manchester United ta amince da farashin £59.7 miliyan domin sayen dan kwallon Real Madrid, Angel Di Maria abinda zai sa ya zama dan wasa mafi tsada a tarihi a Ingila.

Dan kwallon Argentina mai shekaru 26, a yanzu haka yana Manchester United a gwada lafiyarsa kafin ya kulla yarjejeniyar koma wa Old Trafford.

Idan har ya sanya hannun a kwangilar, zai iya buga wasansa na farko tare da tawagar United a tsakaninta da Burnley a ranar Asabar.

Farashin sayen Di Maria ya zarta abinda Chelsea ta biya kan Fernando Torres a shekara ta 2011.

United ta riga ta kashe fan miliyan 72 wajen sayen Luke Shaw da Ander Herrera da kuma Marcos Rojo.

Karin bayani