AFCON: Ethiopia da Kenya sun nuna muradi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kyautar da kasashen Afrika ke kokawa a kai

Kasashen Ethiopia da Kenya sun sanarda bukatar su ta nema damar daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a 2017.

Hakan ya biyo bayan matsayin da Libya ta dauka na janye wa daga batun daukatar bakuncin gasar saboda rikicin da ya rinjabe a kasar abinda kuma ya janyo tsaiko wajen gina filayen wasa.

Ethiopia wacce ta dauki bakuncin gasar a shekarun 1962, 1968 da kuma 1976 ta ce za ta mika bukatar ta nan bada jimawa ba.

Ita kuwa Kenya ta ce tana duba yi wuwar mika bukatar hadin gwiwa tare da Tanzania ko Uganda ko kuma Rwanda.

Hukumar kwallon Afrika CAF ta ce a ranar 30 ga watan Satumba za ta rufe kofar mika takardun neman damar daukar bakuncin gasar.