Bamba ya koma Palermo ta Italiya

Souleymane Bamba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya yi murnar koma wa tamaula a Italiya

Kulob din Palermo na Italiya ya dauko dan kwallon Ivory Coast mai tsaron baya Souleymane Bamba, kan kwantiragin shekaru uku.

Dan wasan mai shekaru 29, kwantiraginsa ne ya kare da kungiyar Trabzonspor ta Turkiya a bara.

Bamba haifaffen Faransa, ya wakilci kasar mahaifansa Ivory Coast a gasar cin kofin Duniya ta matasa a shekarar 2003 da gasar Olympics na 2008 da China ta karbi bakunci.

Dan wasan ya buga wa Ivory Coast dukkan wasannin da ta buga a gasar cin kofin Nahiyar Afirka a shekarun 2010 da 2012, da kuma wasannin gasar kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci.