Lampard ya yi wa Ingila ritaya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lampard ya ce shawara ce mai tsauri a gare shi, don haka sai da ya nutsu kafin ya yanke hukunci

Dan wasan na tsakiya, wanda ya shiga Manchester City aro a kakar bana daga kungiyar New York City, ya buga wa Ingila wasan karshe a matsayin kyaftin inda suka yi canjaras maras ci da Costa Rica a gasar cin kofin duniya na Brazil.

Tsohon dan wasan Chelsea mai shekaru 36 ya buga wasanni 106 tun shigarsa Ingila a shekarar 1999, inda ya bi bayan Steven Gerrard a ritaya daga Ingila.

A karshen kakar wasannin bara ne Chelsea ta saki Lampard, inda ya tafi Amurka gabanin kawo karshen buga wa Ingila wasanni

Dan wasan ya kara da cewa saboda kwallon da yake buga wa kungiyarsa ta yanzu, abu ne mai muhimmanci a gare shi ya tattara hankali a kan iyalinsa kuma ya ba da himma ga nasarar kungiyarsa a nan gaba.