Man United ta kammala cinikin Di Maria

Angel Di Mari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce tun da ya bar Madrid ba kulob da ya kamata ya koma fiye da United

Kulob din Manchester United ya kammala daukar dan kwallon Real Madrid Angel Di Mariya kan kudi sama da fan miliyan 59, a matsayin dan wasan da yafi tsada a tarihin tamaula a Ingila.

Dan kwallon ya rattaba kwantiragi da United na tsawon shekaru biyar ranar Talata.

Di Maria wanda kocin United Louis van Gaal ya kira shi da fitatcen dan kwallon Duniya, ana sa ran zai fara buga wa United wasan da za ta kara da Burnley ranar Asabar.

Kudin da aka sayo Di Maria, ya doke wanda Chelsea ta dauko Fernando Torres daga Liverpool kan fan miliyan 50 a shekarar 2011.

Di Maria ya ce "Louis van Gaal kwararren koci ne kuma fitatce wanda ya samu nasarori da dama, kuma na gamsu da yadda yake kokarin dawo da tagomashin United, don haka nake fatan bada gudunmawa ta".