Milan za ta karbi aron Torres

Fernando Torres Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Torres na fatan dawo da tagomashinsa a Milan

Kulob din AC Milan na Italiya zai karbi aron dan wasan Chelsea Fernando Torres na tsawon zangon kakar wasa daya.

Milan na kokarin maye gurbin Mario Balotelli ne, wanda ya koma kulob din Liverpool kan kudi fam miliyan 16.

Chelsea ta dauko Torres mai shekaru 30 ne a shekarar 2011 kan kudi Fam miliyan 50, inda bai tabuka abin a zo a gani a kulob din ba, kuma dauko Diego Costa da Chelsea ta yi a bana zai rage masa damar haskawa.

Torres ya zura kwallaye biyar ne, a kakar wasan bara, bayan da ya buga wasannin 28.

Haka kuma Milan din ta nuna sha'awar dauko abokin wasan Torres Marco van Ginkel daga Chelsea.