UEFA: Arsenal ta samu tikitin gasar

Alexis Sancheez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption karo na 17 kenan Arsenal na halartar gasar cin kofin zakarun Turai a jere

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai karo na 17 a jere, bayan da ta doke Besiktas ta Turkiya da ci 1-0.

Sabon dan kwallon da Arsenal ta dauko a bana Alexis Sanchez ne ya zura kwallo a raga daf a tafi hutun rabin lokaci.

Arsenal ta samu damar makin lashe wasan tun da wuri, inda 'yan wasanta Santi Cazorla da kuma Alex Oxlade-Chamberlain suka barar da kwallaye.

Saura mintuna 15 a tashi wasa aka bai wa dan kwallon Arsenal Mathieu Debuchy jan kati da hakan yasa ya bar filin wasa.

Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin da aka buga

Athletic de Bilbao - Spain 3 : 1 SSC Napoli - Italy Bayer 04 Leverkusen - Germany 4 : 0 FC Copenhagen - Denmark Malmö FF - Sweden 3 : 0 Red Bull Salzburg - Austria