Benatia zai koma Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mehdi Benatia ya haskaka a Roma a kakar wasan bara

Zakarun kwallon Jamus, Bayern Munich ta cimma yarjejeniyar sayen dan kwallon Morocco Mehdi Benatia daga Roma a kan yawan kudin da ba a bayyana ba.

A cikin wannan makon za a gwada lafiyar Benatia kafin ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da kulob din.

Dan shekaru 27 wanda ya taimakawa Roma ta zama ta biyu a gasar Serie A a kakar wasa ta bara, kuma an yi ta alakantashi da Chelsea da kuma Manchester United.

Tuni Roma ta sayi dan kwallon Olympiakos Kostas Manolas don maye gurbin Benatia.

Bayern na bukatar da wasan bayan, saboda Javi Martinez ya ji raunin da zai hana shi taka leda har sai a cikin sabuwar shekara.