Crystal Palace ta nada sabon koci

Neil Warnock Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Warnock ya taba jagorantar Palace tsakanin shekarun 2007 da 2010

Kulob din Crystal Palace ta nada Neil Warnock a matsayin sabon koci kan kwatiragin shekaru biyu bayan da ya sami fifiko akan tsohon kocin West Brom Steve Clarke.

Dan shekaru 65, Warnorck, wanda ya taba rike Palace tsakanin shekarun 2007 da 2010, zai maye gurbin Tony Pulis bayan da aka cire Malky Mackay a cikin jerin wadanda ake sa ran za a zaba.

Pulis ya ajiye aikinsa ne, kwanaki biyu kafin a shiga sabuwar kakar wasa ta Premier.

Hukumomin Palace sun gayawa Warnock cewa za a sama masa kudaden da zai dauko 'yan wasa kafin a kulle kasuwar musayar 'yan wasan.

A wannan mako aka yi wa Warnock da Clark tambayoyin daukan aiki, bayan da aka cire Mackay, yayin kuma da Tim Sherwood ya fice daga jerin 'yan takarar dake neman jagorantar Palace.