Ingila na daf da nada sabon Kyaftin

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rooney ake sa ran zai gaji Steven Gerrard a Ingila

A ranar Alhamis ake sa ran Ingila za ta bayyana sabon kyaftin din ta wanda zai maye gurbin Steven Gerrard mai shekaru 34, wanda ya yi ritaya.

Dan kwallon Manchester United, Wayne Rooney mai shekaru 28 da haihuwa ake hasashen za a nada sabon kyaftin din tawagar kasar.

Gerrard, kyaftin din Liverpool ya yi ritaya daga buga wa Ingila tamaula a cikin watan Yuli, bayan da aka cire kasar a gasar kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci.

Kulob din United ya nada Rooney sabon kyaftin din kungiyar, inda ya maye gurbin Nemanja Vidic, wanda ya koma buga tamaula a kulob din Inter Milan.

Ingila za ta kara da Norway a wasan sada zumunci a Wembley ranar 3 ga watan Satumba, kafin ta tunkari Switzerland a wasan neman tikikin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai ranar takwas ga watan Satumba.