MK Dons ba ta gigita ni ba-Van Gaal

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Van Gaal ya ce rashin nasarar daukar kofin Capital One abun bacin rai ne

Kocin Manchester United, Louis Van Gaal ya dage cewa bai gigita da casa su da ci 4 da nema ba, a hannun MK Dons ta League One

Van Gaal ya ce ya san hakan tana iya faruwa, don kuwa ba a gina kungiyar kwallo a wata daya.

Kuskuren Jonny Evans ne ya bai wa Will Grigg damar bude ragar Man U, sai kwallo ta biyu wadda dan wasan gaba na MK Dons ya dire ta da kirji, dan wasan aro daga Arsenal, Benik Afobe ne ya sake dama wa Man U lissafi da kwallayensa biyu.

Kocin ya ce sun yi kura-kurai da dama, amma dai ba ya nadamar 'yan wasan da ya sa, ko da yake, akwai kasada a sauye-sauyen da ya yi.

Ya ce "abu ne mai wahala ga magoya baya su amince da falsafata a matsayina na sabon koci, amma abu ne da ya zama dole, don kuwa na zo ne na gina sabuwar kungiya, hakan kuma zai dauki lokaci".