Sai badi Giroud zai koma tamaula

Image caption Tafiyar Giroud jinya, za ta ba wa wasu 'yan wasan gaba na kungiyar dama

Dan wasan gaba na Arsenal, Olivier Giroud ba zai ci gaba da kwallo ba, sai zuwa karshen wannan shekara bayan an dora kafarsa da ta karye.

Kungiyar Arsenal ta karbi sakamakon hoto na biyu da aka dauki kafar Giroud ranar laraba, wanda ya tabbatar cewa dan wasan na kasar Faransa ya karye a idon sawun kafarsa ta hagu.

Giroud mai shekaru 27 ya ji raunin ne, wanda zai hana shi ci gaba da buga wasa tsawon watanni hudu yayin da Arsenal ta kara da Everton a ranar asabar inda suka tashi canjaras 2 da 2.

Kocin kungiyar Arsene Wenger ya ce " Mutane na iya tambayar wa za mu saya don maye gurbin Giroud. A yanzu haka, zan ce musu ba wanda za mu saya."

Dan wasan ya shiga Arsenal ne daga Montpellier a 2012, inda ya buga wasannin kaka guda biyu ya ci kwallaye 16.