Rooney ya zama kyaftin din Ingila

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rooney ya zura kwallaye 40 a wasanni 95

Kocin Ingila Roy Hodgson ya bayyana dan wasan gaban Manchester United Wayne Rooney a matsayin sabon kyaftin din Ingila.

Dan wasan mai shekaru 28, ya karbi kambun daga hannun Steven Gerrard na Liverpool wanda ya yi murabus bayan an cire Ingila a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Rooney ya ci kwallaye 40 a wasanni 95 da ya buga, inda kocin United ya nada shi a kyaftin cikin farkon wannan wata.

Rooney ya rubuta a shafinsa na intanet cewa, "Wannan wani abu ne da zan karba da matukar muhimmanci. Nada ni a matsayin kyaftin ya zarta tunani na."

Ingila za ta kara da Norway a Wembley ranar 3 ga watan Satumba a wasan sada zumunci kafin fara wasanninta na neman gurbi a gasar Euro 2016 ranar 8 ga watan Satumba a Switzerland.