Platini ya fasa takarar shugabancin Fifa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin kwallon kafa na nahiyoyi biyar suna goyon bayan takarar Blatter, ban da Turai

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Uefa Michel Platini ya ce ba zai yi takara da Sepp Blatter don samun shugabancin Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ba.

Bafaranshen mai shekaru 59, ya yi niyyar tsaya wa takara a zaben shugaban Hukumar da za a yi shekara mai zuwa.

Sai dai, Platini ya fada wa wani taron Hukumomin kwallon kafa na kasashen Turai 54 a Monte Carlo ranar alhamis cewa yana son tsai da hankalinsa wajen shugabancin Uefa, ko da yake, a baya ya yi kira da a samu sabbin jini a shugabancin Fifa.

A cikin watan Yuni, Platini ya ce ba ya goyon bayan Blatter, ba ya son ya sake takara, ko da yake ya goyi bayansa a baya, amma nan gaba ba zai mara masa baya ba.

Sepp Blatter, mai shekaru 78, ya fara shugabancin Fifa ne tun a 1998, sai dai yana fuskantar matsin lamba a kan gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar, inda kuma a baya-bayan nan ya nuna sha'awarsa ta sake takara a karo na biyar.

Shawarar Platini na kin takara da Blatter dan kasar Swizerlands na nuna cewa a yanzu mutum daya ne kawai wato tsohon mataimakin babban sakataren Hukumar Jerome Champagne yake takara da Blatter.