Kamaru ta nemi dage wasa da Congo

Kamaru Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamaru za ta kara ne da DR Congo ranar 6 ga watan Satumba

Barazanar cutar Ebola ta sa kasar Kamaru neman dage wasanta da Jamhuriyar Dimokradiyar Congo don samun gurbi a gasar cin kofin Afrika da za a yi a shekarar 2015.

Za a kara tsakanin kasashen biyu ne, ranar 6 ga watan Satumba, Kamaru kuma ita ce kasa ta baya bayan nan da ta gabatar da irin wannan bukata a gaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF.

Wannan bukata ta Kamaru, na zuwa ne bayan da aka samu bullar cutar a kasar ta Jamhuriyt ta Congo, yanzu haka kuma hukumar kwallon kafar ta Kamaru, Fecafoot, ta ce ta na jiran sakamakon wannan bukata da ta mika.

A 'yan kwanakin nan ne hukumar CAF ta umurci kasashen Saliyo da Guniea su mayar da wasannin da za su karbi bakunci zuwa wasu kasashe, inda Guniea za ta kara da Togo a kasar Morocco ranar 6 ga watan Satuma.