UEFA: Liverpool za ta kara da Madrid

UEFA Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta halarci gasar a karon farko cikin shekaru biyar

An fitar da jaddawalin gasar zakarun turai, inda Liverpool wacce ta taba lashe kofin karo biyar ta tsinci kanta a rukuni na biyu da ke dauke da Real Madrid wacce ke rike da kofin gasar.

Liverpool za ta kara ne a gasar a karon farko cikin shekaru biyar, bayan rashin halartar wasan da ta yi fama da shi.

Atletico Madrid na rukunin farko tare da Juventus da Olympiakos.

Haka kuma an saka Manchester City a rukunin na biyar da ke dauke da Bayern Munich yayin da Arsenal da Borussia Dortmund suka kasance a cikin rukuni na hudu.

Chelsea dai na rukuni na bakwai ne, wanda ke dauke da kungiyar Sporting Lisbon ta Portugal.