Xabi Alonso ya koma Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kakarsa ta farko ya lashe gasar zakarun Turai a kungiyar Liverpool

Bayern Munich ta amince ta sanya hannu a kan kwantiragin shekaru biyu da dan wasan tsakiya Xabi Alonso daga kungiyar Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 32, ya shafe tsawon shekaru biyar a Madrid bayan sayen shi daga Liverpool a kan fam miliyan 30 a shekara ta 2009.

Dan kasar Spaniyan, wanda ya lashe gasar zakarun Turai a kakar bara, ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru biyu ne kawai da kungiyar a wata Janairu.

Xavi Alonso ya sanar da yi wa kasar ritaya daga kwallo ranar laraba da ta wuce bayan ya buga wasanni 114.

Dan wasan ya yi gwajin lafiya, ranar alhamis, kuma a juma'ar nan ne ake sa ran zai yi jawabi ga maneman labarai a kan yunkurin komawarsa Munich.

Alonso, wanda ya ci gasar zakarun kasashen Turai guda biyu da kofin duniya, ya fara taka leda a Real Sociedad kafin ya koma Liverpool a 2004, inda ya lashe gasar zakarun Turai.