Leicester ta rike Arsenal wasa 1-1

Leicester Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana matsayi na 5 a teburin Premier bana

Kungiyar Arsenal ta tashi wasa 1-1 da Leicester a gasar cin kofin Premier wasan mako na uku da suka kara a King Power Stadium ranar Lahadi.

Alexis Sanchez ne ya fara zura wa Arsenal kwallo, bayan da ya tsinci tamaula a sadaka lokacin da Yaya Sanogo ya yi kokarin buga kwallo ta gefan gola Kasper Schmeichel.

Sai dai minti biyu tsakani Leicester karkashin koci Nigel Pearson, ta farke kwallonta ta hannun Ulloa bayan da ya sawa kwallo kai ta wuce gola Laurent Koscielny.

Leicester ta samu damarmakin kara kwallaye ta hannun Ulloa da Jamie Vardy wanda ya shigo wasa sauyin dan kwallo.

Arsenal tana matsayi na bakwai a teburin Premier bayan wasanni uku da maki 5, yayin da Leicester ke mataki na 15.