CAF ta kori daukaka karar Rwanda

Caf Logo Hakkin mallakar hoto
Image caption Congo ce za ta maye gurbin Rwanda a rukunin farko

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Afirka CAF ta kori daukaka karar da Rwanda ta shigar saboda korarta da aka yi daga wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na 2015.

Hakan na nufin Congo Brazzaville za ta fafata a rukunin farko domin neman tikitin da mai rike da kofin Nigeria da Afirka ta Kudu da Sudan.

CAF, ta kori Rwanda daga wasannin ne a zagaye na biyu, bisa takaddama kan dan wasanta Daddy Birori wanda Congo ta shigar da karar cewar dan kwallon bai kamata ya buga wasan ba.

Dan wasan dai yana da passports na Rwanda da Congo wanda suke dauke da sunaye da kuma shekaru daban-daban.

CAF ta sanar da cewar kundin tsarin wasanninta ya ce "Duk tawagar da ta bada bayanan dan wasa na karya....... za a kori kasar daga gasar".