AFCON: Saliyo da Congo a Lubumbashi

Ebola Strike Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption CAF na kokarin kaucewa kamuwa da cutar kwayar Ebola

Saliyo za ta karbi bakuncin karawar da za tayi a wasan neman tikitin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka da Congo a Lubumbashi Jamhuriyar Congo ranar 10 ga watan Satumba.

Tun farko Saliyo ce ya kamata ta karbi bakuncin wasan a Freetown, amma hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta dauke wasan saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.

Tuni kasar Saliyo ta dakatar da wasannin kwallon kafa a kasar, tun kafin CAF ta bada sanarwar dauke wasan da za ta karbi bakuncin Congo.

Sakatare janar na hukumar kwallon Saliyo ya ce "A kasar Congo za mu buga wasa mu kuma karbi bakuncinsu a kasarsu, mun gode wa kasar yadda muka sanar da su shirin mu suka kuma amince mana da gaggawa".

"Sai dai sun bamu ka'idoji, daya daga ciki shi ne dukkan tawagar da za ta isa kasar daga Saliyo sai anyi musu gwajin kwayar cutar Ebola da tabbacin lafiyarsu".