Liverpool ta doke Tottenham 3-0

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana matsayi na 5 da maki 6 a teburin Premier

Kocin Liverpool Brenda Rodgers ya jagoranci kulob din a wasansa na 100 da kungiyar, inda ya doke Tottenham da ci 3-0 a filin wasa na White Hart Lane.

Raheem Sterling ne ya fara zura kwallo a ragar Tottenham a minti na takwas da fara wasa, kuma haka aka tafi hutu Liverpool nada kwallo daya a raga.

Bayan an dawo daga hutu Liverpool ta samu bugun fenarity, inda kyaftin Steven Gerrard ya zura kwallo a raga a minti na 49, kuma fenarity na 45 da ya ci kwallo a Liverpool.

Mario Balotelli ya barar da damarmakin zura kwallo a raga a wasan farko da ya buga wa Liverpool tamaula, kafin daga baya Alberto Moreno ya zura kwallo ta uku a raga a mintuna na 60.

Kakar wasa ta bara a dai-dai wannan lokacin, kwallaye biyar Liverpool ta zura a ragar Tottenham, kafin ta casa ta 4-0 a gidanta.