Man United ta amince da farashin Blind

Daley Blind Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan kwallo na biyar da United ta dauko a kakar bana

Kulob din Manchester United ya amince da farashin Daley Blind dan kwallon Netherlands mai wasa a kungiyar Ajax kan kudi sama da fam miliyan 13.

Blind, mai shekaru 24 yana cikin tawagar koci Louis van Gaal da suka buga gasar kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci.

Dan kwallon yana tsaron baya ta hagu, kuma zai iya tsaron baya ta tsakiya, wanda tuni ya isa United domin duba lafiyarsa.

Blind, shi ne dan kwallo na biyar da United ta dauko a bana, ciki har da Angel Di Maria daga Real Madrid wanda aka sayo mafi tsada a tarihin kwallon Ingila.

United ta kashe sama da fam miliyan 130 wajen sayo Luke Shaw da Ander Herrera da Di Maria da kuma Marcos Rojo.