Kagawa ya koma Borussia Dortmund

Shinji Kagawa Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Kagawa ya ce yaso ya nuna kansa a gasar Premier

Dan kwallon Manchester United Shinji Kagawa, ya sake koma wa Borussia Dortmund sai dai ba a bayyana kudin da aka sayi dan wasan ba.

Dan wasan mai shekaru 25 ya rattaba kwantiragin shekaru hudu, kulob din da ya buga wa tamaula a shekarar 2010 zuwa 2012 kafin ya koma United kan kudi fam miliyan 12.

Wasa daya ya buga wa United karkashin jagorancin Louis van Gaal a karawar da MK Dons ta doke United 4-0 a kofin Capital One.

Kagawa ya koma Dortmund daga Cerezo Osaka, inda ya buga wasanni 61, ya kuma zura kwallaye 24 a raga.

Ya kuma bar United mako guda da kungiyar ta dauko Angel Di Maria daga Real Madrid kan kudi sama da fam miliyan 59, a dan kwallon da yafi tsada a tarihin tamaular Ingila.