Real Sociedad ta doke Madrid da ci 4-2

Sociedad Madrid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Madrid za ta karbi bakuncin Athletico Madrid a wasan mako na uku

Kulob din Real Sociedad ya doke Real Madrid da ci 4-2 a gasar cin kofin La Ligar Spaniya a wasan mako na biyu da suka kara ranar Lahadi.

Ramos ne ya fara zura kwallo a ragar Sociedad minti na biyar da fara tamaula, kafin Gareth Bale ya kara kwallo ta biyu a minti na 11.

Sociedad ta rage kwallon farko a minti na 35 ta hannun dan wasanta Iñigo Martínez, ta kuma zare kwallo ta biyu saura minti hudu a tafi hutun rabin lokaci ta hannun Zurutuza.

Bayan da wasa ya koma 2-2 aka kai mintuna na 65 ana fafatawa sai Zurutuza ya samu dama ya kuma zura kwallo ta uku a ragar Madrid, kafin Vela ya kara kwallo ta hudu a mintuna na 75.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Atletico de Madrid a wasan mako na uku a Bernabeu, yayinda Celta de Vigo za ta kara da Real Sociedad a filin Municipal de Balaidos.