Nigeria za ta kai karar Schalke wajen FIFA

Chinedu Obasi Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria za ta kai karar kungiyar kwallon kafa ta Schalke da ke Jamus wajen FIFA, bayan kulob din ya ki ya kyale dan wasan Nigeria Chinedu Obasi ya buga mata a wasan neman shiga gasar cin kofin kwallon nahiyar Afrika da za a yi a wannan watan.

Kulob din Schalke ya daura laifin hakan a kan cewa, an rike fasfo din dan wasa Obasi ne a wani ofishin jakadanci, a wani bangare na shirye-shiryen da suke yi na karawa a gasar cin kofin zakaru na nahiyar turai.

Sai dai mai magana da yawun tawagar Super Eagles ta Nigeria Ben Alaiya, ya ce "muna da wasanni biyu da FIFA ta amince da ranakun buga su, kuma mu ne muka fi cancantar ya buga wa idan hakan ta kasance".

'Yan kwallon Super Eagles na Nigeria wadanda su ke rike da kofin nahiyar Afrika, za su kara ne da Congo a ranar 6 ga watan Satumba, sannan su kara da Afrika ta Kudu kwanakin hudu bayan hakan.

Ben Alaiya ya ce a yanzu Nigeria za ta kai kara wajen Fifa domin ta dauki mataki kan kulob din na Schalke.

Karin bayani