Arsenal ta amince da farashin Welbeck

Danny Welbeck
Image caption Giroud zai yi jinyar rauni na tsawon watanni hudu

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta amince da farashin dan kwallon Manchester United Danny Welbeck kan kudi fam miliyan 16.

United ce ta sanar da Welbeck cewar zai iya barin kulob din tun da ta dauko Radamel Falcao aro daga kungiyar Monaco.

Dan wasan Ingila mai shekaru 23 da haihuwa, United ce ta bashi izinin barin Otal din da suke a Watford domin ya je Arsenal ya cimma yarje-jeniya da kulob din.

Arsenal ta dade tana zawarcin dan wasa mai zura kwallo a raga, tun lokacin da Oliver Giroud ya karye a kafarsa da zai yi jinyar watanni hudu.