Feyenoord ta dauko Karim El Ahmadi

El Ahmadi Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan ya ce zai haskaka a gasar Netherlands

Feyenoord ta dauko dan kwallon Aston Villa dan wasan Morocco Karim El Ahmadi kan kwantiragin shekarun uku.

Mai shekaru 29 da haihuwa, ya buga wa kulob din Netherlands tamaula a shekarun 2008 zuwa 2012, kafin ya koma Al Ahli ta hadaddiyar daular labarawa wasa aro a shekarar 2011.

Shi ne dan wasa na farko da kocin Villa Paul Lambert ya dauko a shekarar 2012.

El Ahmadi ya ce "Na sha fada a baya, zan koma kwallo Feyenoord komai dade wa.