Falcao ya koma Manchester United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Radamel Falcao ya haskaka a Spain a shekara ta 2012

Manchester United ta amince da sayen dan kwallon Colombia, Radamel Falcao a matsayin aro daga kungiyar Monaco ta Faransa.

Dan shekaru 28, za a gwada lafiyarsa a United kafin a kulla yarjejeniyar.

Tun daga bude kasuwar musayar 'yan kwallo a bazara ake bayyana cewar Falcao zai bar Monaco ya koma gasar wata kungiya ko a Spain ko a Ingila.

A cikin watan Mayun 2013, Falcao ya koma Monaco daga Atletico Madrid a kan fan miliyan 50.

Ya zura kwallaye 11 a cikin wasanni 20 tare da Monaco.

Karin bayani