Hull ta dauko Hernandez mafi tsada

Abel Hernandez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasa na bakwai kenan da Hull City ta dauko a bana

Kulob din Hull City ya dauko Abel Hernandez dan kwallon Uruguay daga kungiyar Palermo a dan wasan da ta sayo mafi tsada a tarihin kungiyar da ya kai fam miliyan 10.

Dan wasan mai shekarun 24 da haihuwa, ya rattaba kwantiragin shekaru uku da Tigers da kuma zabin kara masa wata kwantiragin shekara guda.

Hernandez shi ne dan wasa na bakwai da Hull ta dauko a bana, ya buga wa Uruguay wasanni 14, ya kuma zura kwallaye bakwai, ya kuma buga wasanni biyu a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil.

Dan wasan ya zura kwallaye 14 daga cikin wasanni 28 da ya buga wa Pelermo, wanda ya taimaka wa kulob din koma wa gasar Seria A a bara.

Hull ta samu damar sayen dan kwallon ne bayan da ta sayar da Shane Long ga kungiyar Southampton kan kudi fam miliyan 12.