Micah Richards ya koma Fiorentina

Micah Richards Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Richards yana son ya dinga buga wasa akai-akai

Dan kwallon Manchester City Micah Richards zai kawo karshen zamansa a kulob din shekaru 12, inda zai koma Fiorentina buga tamaula aro.

Richards, mai shekaru 26 da haihuwa, zai zama dan kwallon Ingila na 24 da zai yi wasa a gasar Serie a ta Italiya.

Kungiyoyin Premier da dama sun yi zawarcin dan kwallon, amma ya amince ya koma Fiorentina wasa aro, da nufin kulob din ya saye shi daga baya idan ya taka rawar gani.

Dan wasan ya koma City ne yana da shekaru 14 da haihuwa, ya kuma fara buda wasan Premier a watan Oktoban shekarar 2005.

Richards, wanda ya buga wa City wasanni sama da 250, ya amince ya bar kulob din ne da nufin samun damar buga wa wata kungiyar wasanni akai-akai.

City za ta sake rabuwa da wasu 'yan kwallon domin cika ka'idar hukumar Turai, kan yawan 'yan wasa a kungiya da kudaden da za a dinda biyansu.