Hernandez ya koma Madrid wasa aro

Javier Hernande Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid tana da zabin sayen dan kwallon

Dan kwallon Manchester United Javier Hernandez ya koma Real Madrid wasa aro na tsawon kakar bana.

Real Madrid tana da zabin sayen dan kwallon mai shekaru 26, wanda ya koma United daga kulob din Guadalajara a shekarar 2010.

Dan wasan Mexico ya bar United ne saboda kulob din ya dauko Radamel Falcao aro daga Monaco.

Hernandez zai zama mai jiran kar ta kwana a Madrid idan Karim Benzema ya gamu da matsala a Bernabeu.

Dan kwallon ya zura kwallaye 20 a kakar farko da ya fara buga wa United tamaula, ya zura kwallaye 37 jumulla a wasanni 102 da ya buga wa kungiyar.