NFF:Giwa ya yi watsi da barazanar FIFA

NFF LOGO Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daren yau ne wa'adin Giwa zai cika, kafin hukuncin FIFA ranar Talata

Sabon shugaban hukumar kwallon kafar Nigeria Chris Giwa, ya yi watsi da kurarin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, cewa za ta dakatar da kasar daga shiga harkar kwallon kafa.

Giwa ya karbi ragamar shugabancin NFF ne Talatar da ta gabata, bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a lokacin da jami'an tsaro su ka gayyaci tsohon shugaban hukumar Aminu Maigari don amsa tambayoyi.

Sai dai bangaren Aminu Maigari sun yi watsi da zaben, suka kuma tsaida ranar 4 ga watan Satumba domin gudanar da sabon zaben hukumar NFF.

FIFA ta rubutawa sabon shugaban da jami'ansa da su bar kujerar da suka dare kafin daren Litinin, ko kuma a saka wa hukumar takunkumi ciki har da dakatar da kasar shiga harkokin tamaula.

Giwa ya ce "Mun ga wasikar da FIFA ta rubuta da dukkan abin da ta kunsa, iya sani na babu abinda zai sauya, za mu gabatar da matsayin mu ga FIFA, kuma ina da tabbacin za su saurare mu su kuma amince da mu".

Dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa zai kawo wa kasar koma baya a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, wanda kasar ce ke rike da kofin.

Sai dai Giwa ya kara da cewa "Muna kira ga 'yan Nigeria kada kowa ya razana, ba za a ci mutuncin NFF ba, bama tsammani za a saka mana takunkumi domin mun bi dukkan ka'idoji, saboda haka surutai kawai ake yi".

Tun lokacin da aka kammala gasar cin kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci hukumar NFF ta shiga rikita-rikita, inda wata kotu ta kori Maigari daga kujerarsa kuma jami'an gwamnati suka dare mulki.

Daga baya kotun ta dawo da Maigari kan aikinsa, sai dai kwamitin amintattu na NFF ya sauke shugaban bisa zarginsa da cin hanci da almundahana.

FIFA ce ta shiga tsakani, inda tace ba a bi ka'idoji ba wajen cire shugaban, ta kuma umurci da a gudanar da shirye- shiryen sabon zabe.