Wenger: Damu za a ci gaba da damawa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsene Wenger na fuskantar matsin lamba kan dan wasan gaba

Kungiyoyin kwallon kafa a Ingila, na ta fafutukar ganin cewa sun kammala dauko 'yan wasa yayin da wa'adin da aka diba na yin hakan ke shirin cika a yau Litinin.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger na daya daga cikin masu horar da 'yan wasan da ke ta fadi tashin ganin ya dauko sabon dan wasan gaba yayin da yake fuskantar matsin lamba daga magoya bayan kulob din kan maye gurbin Olivier Giroud wanda ke fama da jinya.

"Mun dukufa wajen ganin cewa mun samu mafita, babu wanda zai iya hasashen ko me zai faru nan da sa'oi 24 msu zuwa", In ji Wenger.

Da karfe 11 daren yau ne ake sa ran za a rufe kasuwar daukan 'yan wasan yayin da kididdiga ta nuna cewa izuwa yanzu an kashe akalla fam miliyan 725 wajen musayar 'yan wasa a gasar Premier ta Ingila.

Karin bayani