Azpilicueta ya tsawaita kwantiragi da Chelsea

Cesar Azpilicueta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce ya yi murnar tsawaita kwantiraginsa da kulob din

Dan kwallon Chelsea mai tsaron baya Cesar Azpilicueta, ya tsawaita kwantiraginsa da kulub din na tsawon shekaru biyar.

Dan kwallon Spaniya mai shekaru 25, ya buga wa kungiyar wasanni 95, tun lokacin da ya koma kulob din daga Marseille kan kudi sama da fam miliyan shida.

Azpilicueta ya koma Chelsea ne a shekarar 2012, inda ya taimakawa kulob din lashe kofin zakarun Turai wato Europa League a shekarar 2013.

Dan wasan ya buga wa Chelsea wasanni uku da ta buga a gasar Premier bana, wanda ta ke matsayi na daya a teburin Premier.

Kungiyar ta sanar a shafinta na intanet ce wa "Tana farin cikin sanar da cewa Cesar Azpilicueta ya tsawaita kwantiraginsa na tsawon shekaru biyar".