Jamus ta nada Schweinsteiger kyaftin

Bastian Schweinsteiger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan yana jinyar rauni da ya ji a gwiwar kafarsa

Kocin kungiyar kwallon kafar Jamus Joachim Loew ya nada Bastian Schweinsteiger a matsayin sabon kyaftin din tawagar 'yan wasan kwallon kafar kasar.

Schweinsteiger mai kwallo a Bayern Munich ya maye gurbin Philip Lahm, wanda ya yi ritaya bayan gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil.

Loew ya ce "Bastian kwararren dan kwallo ne, wanda zai iya jan ragamar tawagar 'yan wasa da kasarmu za ta ci gaba da yin fice a harkar tamaula".

Dan wasan wanda ya buga wa Jamus wasanni 108, yana jinyar rauni da ya ji a gwiwarsa, inda golan Munich Manuel Neuer zai shugabanci 'yan wasa a karawar da za su yi da Argentina a wasan sada zumunci a Dusseldorf ranar Laraba.

Haka kuma kocin Jamus ya sanar da nada tsohon kocin Stuttgart Thomas Schneider a matsayin mataimakinsa, domin maye gurbin Hansi Flick wanda ya koma Daraktan wasanni a hukumar kwallon kafar Jamus.

Kocin Jamus ya ce a duk lokacin da sabon kyaftin bai samu damar buga mana wasa ba, akwai zakakuren 'yan kwallo da za su ja ragamar 'yan wasanmu da suka hada da Neuer da Sami Khedira da Thomas Mueller da Mats Hummels.