AFCON: Ivory Coast za ta kara da Saliyo

Ivory Coast Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ivory Coast ta amince za ta kara da Saliyo ranar Asabar

Ivory Coast za ta karbi bakuncin Saliyo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na badi ranar Asabar.

Tun farko gwamnatin Ivory Coast ce ta ce ba za ta karbi bakuncin Saliyo ba, saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.

Saliyo na daya daga cikin kasashe shida a Afirka da ke fama da cutar Ebola, har ma ta dakatar da wasan kwallon kafa a kasar.

A kokarin da take na hana yaduwar cutar, gwamnatin Ivory Coast ta soke karbar bakuncin wasanni tsakanin kasashe.

Sai dai kasar ta karbi bakuncin gasar cin kofin zakarun Nahiyar Afirka wato Confederation cup da wasan share fage na gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekaru 20.

Tun a baya hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta shaida wa kasar cewar idan ba ta karbi bakuncin wasan ba, za a yi mata hukuncin da zai hada da korarta daga wasannin neman shiga gasar kofin Nahiyar Afirka.

Sauran kasashen da ke rukunin da za su fafata sun hada da Jamhuriyar Congo da Kamaru a rukuni na hudu.