'Arsenal ce ta makara daukar Falcao'

Radamel Falcao Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption United tana da zabin sayen dan kwallon idan ya yi mata

Mahaifin Radamel Falcao ya ce kulob din Arsenal ne ya makara daukar dan wasan, wanda Liverpool da Manchester City da Juventus duk suka yi zawarcinsa.

An yi ta rade-radin cewa Falcao, mai shekaru 28 dan kwallon Colombia, zai koma Real Madrid ta Spaniya zai koma tamaula kafin Manchester United ta dauko dan kwallon.

Radamel Garcia ya sanar da wata kafar yada labarai a Colombia cewa "Kungiyoyin da suka yi zawarcin dansa sune Juventus da Manchester City da Liverpool kafin Arsenal da ta nemi dan wasan a kurarren lokaci".

"Real Madrid tun farko cewa ta yi a kai kasuwa kafin daga baya Manchester United ta amince ta dauki dan kwallon".

Falcao ya koma Monaco a kan kudi fam miliyan 50 daga kulob din Atletico Madrid a Yulin 2013, inda ya buga mata wasanni 20 ya zura kwallaye 11 a raga.